![]() |
| Details from police |
Da ya ke zantawa da manema labarai a yau Alhamis, Kwamishinan Ƴan sanda, Hussain Gumel, ya ce an kama wanda ake zargin ne a Sabon Birni a ranar 10 ga watan Oktoba, bayan samun sahihan bayanai.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ba zai iya bada bayanin yadda ya samu katikan ba.
“Ana zaton cewa masu wadannan katunan ba ƴan karamar hukumar Sabon Birni ne kadai ba, za su iya fitowa daga sassan jihar saboda ba mu iya gano wadanda suka mallaki katinan PVC ɗin ba,” inji shi.
Sai dai ya yi kira ga jama’a, musamman wadanda katinan su ya ɓace ko kuma su zo hedikwatar hukumar su duba.
CP ɗin ya kuma ce ƴan sanda za su mayar da duk katinan da ba a karba ba ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) bayan wata ɗaya.
