Dan Kasar Chaina ya musanta hallaka Marigayiya Ummita

Mazaunin Kano, Mista Geng Quangrong ɗan asalin ƙasar Sin da ake zargi da hallaka tsohuwar budurwarsa Ummukhulsum Sani Buhari da aka fi sani da Ummita, ya musanta zargin cewa shi ne ya kashe ta.

Ɗan kasuwar ya musanta hakan ne bayan da aka sake gurfanar da shi a gaban kotu a jiya Alhamis.

Rahotanni sun ruwaito cewa, Bayan karanto masa zargin a babbar kotun Kano, Mista Geng Quangrong ya ce, zargin da ake yi masan ba gaskiya ba ne.

Hazalika Mista Guo Cunru, shi ne mutumin da ofishin jakadancin China a Nijeriya ya turo don ya yi wa wanda ake zargin tafinta daga turancin Ingilishi zuwa harshen Chinanci.

Lauya mai gabatar da kara wanda kuma shi ne kwamishinan Shari’a na Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya bukaci kotun ta fara sauraren tuhumar da ake yi wa wanda ake zargin.

Alkalin babbar kotun Shari’a Sanusi Ado Ma’aji ya ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 16 ga watan gobe na Nuwamba domin gabatar da shaidun da masu kara suka za su kawo.

Idan za a iya tunawa dai, Ana zargin Mista Geng da kutsa kai cikin ɗakin Ummita tare da caka mata wuƙa a gidansu da ke unguwar Jan Bulo da ke Kano a watan Satumba.

Inuwar Labarai 

Post a Comment

Previous Post Next Post