Hukumar kashe gobara ta jihar Kano, ta tabbatar rasuwar wani magidanci Malam Habibu Mu’azu mai shekaru 45 a garin ƴan dutse da ke yankin ƙaramar hukumar Bichi.
Jami’in hulɗa da jami’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ne bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Juma’a.
Sanarwar ta ruwaito cewa jami’an hukumar ƙaramar hukumar ta Bichi ne suka karɓi kiran gaggawa da misalin ƙarfe 07:44 na safe daga wani mai suna Malam Sanusi Abubakar inda ya sanar da su faɗawa Rijiyar da mutumin ya yi.
Sanarwar jami’in ta ce, “Bayan isar jami’anmu wurin da misalin ƙarfe 8:20 na safe, sun fito da shi ba ya cikin hayyacin sa, kuma bayan kai shi asibiti likita ya tabbatar da rasuwarsa.”
“Tuni hukumar mu ta miƙa gawarsa ga dagacin garin na Ƴan Dutse Malam Bello Usman, kuma muna ci gaba da binciken musabbabin faruwar lamarin, Inji mai magana da yawun hukumar ta kashe gobara ta jihar Kano.

