Ɗan takarar shugabancin Najeriya a majalisar NNPP, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce ba shi da wata niyya na janye takarar da yake yi kamar yadda wasu ke zargi.
Kwankwaso ya yi wannan martani ne ga waɗanda suke ganin jam’iyyar sa da takarar sa bata da ingancin da za a zaɓe shi a kakar zaɓen 2023.
Kwankwaso ta cikin wata tattaunawa da yayi da wakilin Rfi Hausa ya ce “PDP da APC jam’iyyu ne da suka ruɓe, al’ummar ƙasa sun dawo daga rakiyar su, babu wata masalaha ga ɗan Nijeriya sama da zaɓen mu domin mu gyara abinda jam’iyyun nan suka ɓata”.
Daga nan ne ya musanta zargin da ake yi yana rufe ƙofa da Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda kwankwaso ya ce “Bana wani zama da Gwamnan Kano, kuma babu wannan maganar”.
Sannan ya zargin ƙungiyar dattawan arewa, ya ce tun da wannan ƙungiya ta sauka daga layin da take ta shiga siyasa, a shirye suke da su fatattaka ta nan gaba.

