Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)
Rundunar Sojojin Najeriya sun kawar da 'yan ta'addar ISWAP da dama da jiragen yaki, inda suka jefa bama-bamai a sansanonin 'yan ta'addan dake yankin Damboa na jihar Borno.
Zagazola ya bayar da rahoton cewa "An kai wasu hare-hare ta sama da dama daga rundunar sojojin sama na Operation Hadin Kai a ranar 27 ga watan Nuwamba 2022 yayin da aka kai wa ayarin motocin 'yan ta’adda hari".
Ya cigaba da cewa "...gawawwakin 'yan ta'addan sun watse a ko'ina a yayin da 'yan ta'addan da suka tsira suka yi ta kai ruwa rana".
Majiyar ta lashi takobin cewa rundunar sojojin saman Najeriya za su cigaba da kai farmakin da suke kai wa a kan 'yan ta’addan a yankin Arewa maso gabas.
Inuwar Labarai RPT 001
Tags:
TA'ADDANCI
