![]() |
| Details From KANYWOOD |
Wakilin Jaridar Inuwar Labarai a Kano Ibrahim Hamisu ya samu tattaunawa dashi.
Ga yadda Sanarwar ta kasance.
Za mu so ka gabatar mana da kanka ga masu karatunmu?
Suna na mas'ud Umar (m.m.sidi)
Ko za ka ba ba mu to takaitaccen tarihinka ?
An haifeni a unguwar gwammaja layin malam Rabi'u Usman Baba, nayi primary, na tafi secondary ban kai ga kammalawa ba mahaifina ya umarceni da in koma Islamiyya domin samun hadda ta alqur'ani, kuma Alhamdulillah na sami gwargwadon abinda na samu na Qur'ani wanda naci gaba da koyarwa a makarantar da nayi karatu, har Allah ya hadani da matar da na aura wacce daya ce daga cikin dalibai na, yanzu muna da yara uku da ita.
Ta yaya aka samu kai a masana'atar Fim ta Kannywood?
Na fara ne daga zuwa kallon drama wata kungiya da suke wasan kwaikwayo na dabe da wasan chanis wato Dabo Film association, tun ina zuwa ana korata shekaruna basu kai ba, har wataran na tarar Shugaban kungiyar kabiru na kwango yana bayanin yadda ake register da kungiyar daga rannan nima na sai form nayi register da kungiyar na fara, dama kuma burina a duniya tin cikin yarinta ina cewa abokaina in na girma nai kudi sai naje India an nunoni a TV, hakan yasa da naga abin a kusa da ni nace burina zai cika.
A wace shekara ka fara Fim?
Idan aka cire tsawon lokacin dana kwashe ina drama na fara film gadan gadan daga shekarar 2013, shekara 9 kenan.
A wane Fim ka fara fitowa?
Na fara da wani film Mai suna AHADI Wanda na fito a matsayin wani karamin yaro da yake girma ya zama shehu Hassan Kano.
Daga lokacin da fara zuwa yanzu Finafinai nawa zaka iya cewa ka fito?
Tirkashi, gaskiya da yawa, amma Finafinan da na taka rawa a matsayin jarumi za su kai 20 banda Special appearing, ga wasu daga ciki: HAKURI DA RASHINSA Wanda megida na farko a masana'antar film Ali Rabiu Ali Daddy ya shirya min, ga kadan daga cikin wadan da na fito aciki sun hada da: HAKURI DA RASHINSA, DABI'AR ZUCIYA, DADIN ZAMA, CAMFI, HALIN SO, MIJIN AURE, KWANA CASAIN, DADINKOWA. Da sauransu.
Amma wadan da ni na bada umarni za su kai akalla guda 9 zuwa 10, ga kadan daga ciki: SO BAYAN AURE, MATAN KIRKI, ZUMA DA MADACI, DAURIN ZATO, JININ MAHAIFIYATA.
Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu wadanne nasarori za ka iya cewa ka samu?
Alhamdulillah na sami nasarori masu tarin yawa, na farko na cika mafarkina domin duniya ta karbeni a matsayin jarumi, sannan na sami rufin asiri daidai gwargwadon abinda Allah ya kaddara min gaskiya dai Alhamdulillah.
Kalubale fa akwai ko Babu?
Gaskiya nasha kalubale tin a karin farko kasancewar mahaifina malamin alqur'ani ne, don haka yan uwana an yi ta yi min suruta cewa na saki tarbiyyar gidanmu na hau wata hanya ta lalacewa, na sha wuya matuka kafin a fahimceni, nasha yin kudurin zan hakura Dan kar in batawa mahaifana da asalina amma abin ya gagara, Wanda yana daga cikin dalilan da yasa mahaifina ya maida karatuna bangaren qur'ani da addini, har zuwa lokacin da Allah yasa suka fahimci waye dansu kuma sukai min addu'a da fatan Alheri da nasihar kar inyi wani abu da ya sabawa addini na da al'adata,
Wane ne allon kwaikwayonka a Kannywood?
Allon kwaikwayo na Kabiru na kwango. A bangaren rubutu kuma Nazir Adam salihi, shi ne marubucina kuma ina kokarin kwatanta irin salon yadda yake rubutunsa, duk da cewa daga baya kasancewa ta da Ali Rabiu Ali Daddy wanda shi ne mai gidana.
Wane Fim ne ya fi baka wahala?
Gaskiya film din ZUMA DA MADACI shi ne film din da yafi ba ni wahala matuka, ban taba yin aikin da ya bani wahala kamar shi ba, kuma Alhamdulillah ya sami nasarori masu tarin yawa da kuma kalubalen da bazan taba mantawa da shi ba.
Mene ne burinka a wannan masana'anta ta Kannywood?
Burina a gaskiya shi ne Allah ya kawo lokacin da zan dangane da Hollywood domin yin aiki tare dasu.
Wace shawara zaka baiwa masu sha'awar fara yin Fim?
To shawarar da zan bawa masu sha'awar shiga film tun a farko ya kamata su zama masu manufa me kyau wajan shiga film, ya zama manufar su ta Alkhairi ce, sannan su bi matakai da kungiyoyin shiga film suka shimfida wajan shiga, sannan su daura damarar juriya da hakuri da biyayya, indai sukai haka insha Allah za su cimma burinsu.
Tags:
KANNYWOOD


