Kungiyar Malaman Tsangayun Jihar Borno Su Ma Sun Yi Kira Ga Mambobinsu Kan Zaben Shugabanni Na Gari.

Kungiyar Malaman Tsangaya Reshen Jihar Borno ta gudanar da babban Taron ta na wuni guda domin karfafa membobinta wajen Zaben Shugabanni Na gari.

Taron daya samu halarta membobi daga Kananan Hukumomi 27 na Jihar gami da baki daga jihohin Yobe,Adamawa,Taraba da Gombe.

Dayake Jawabi Shugaban Kungiyar na Kasa Gwani Ibrahim Abubakar Mai Bindiga ya nuna matukar farin cikinsa Kan goyon baya da hadin Kai da membobinmu suke bamu.

A yanzu Kungiyar Malaman Tsanagayu ta maida hankali Kan dawo da martabar makaranta dama Almajirai domin samu dukkan Yanci Kamar yadda dokar kasa ta tanajar.


Gwani ya Kara da cewa An San Almajirai da bin doka da oda don haka muke Kira ga yan siyasa da su Sani Wanda zasu cika Mana alkawuran da suka Mana zamu zaba a Zaben 2023.

Dayake nasa Jawabi Shugaban Kungiyar Reshen Jihar Borno Gwani Usman Abdullahi ya nuna farin cikinsa ganin Irin Nisan zangon da Shugaban Kungiyar na Kasa ta tako domin halarta wannan taro.

Gwani Usman ya Kara da cewa a yanzu kuri'u sun zama makamin da zaa iya chanja Shugabanni masu adalci.

Gwani ya Kara da cewa zuwa yanzu Suna da adadin Almajirai da Malamai dubu Dari biyu da Sha daya da talatin da uku Wanda suke shirya tsaf domin kada Zabe ga Wanda Shugabanni Kungiyar ya bada umarni.

A nasa Jawabi Malami A jami'ar Sule Lamido dake Kafin Hausa Dr.Abubakar Maje ya kawo Irin nasarar da Kungiyar ta Sami gani cewa a yanzu kudirin Almajirai yana gaban majalisar tarayya domin karatu na biyu.

Dr.Abubakar ya Kara da cewa muna so zuwa gaba ya zama Ana bawa Malamai da Almajirai shedar Kammala karatu Wanda zasu iya amfani da ita a koina a fadin duniya .

A karshe Dr.Abubakar ya sake Kira ga membobin Kungiyar da su cigaba da zamanto masu bin doka da oda Kamar yadda akasan makarantar Tsangaya tana dashi.

Post a Comment

Previous Post Next Post