Magidanci Ya Saki Matarshi A Sakamakon Kamata Tana Chatting Da Makobcinsu A Jihar Lagos.

Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

Wani miji ya kama matanshi tana chatin da makobcinsu wanda hakan yayi sanadiyan mutuwan aurensu.

Magidancin ya bukaci kotu da ta raba aurensu da matanshi bisa zargin ta da cin amanan aure da yin hira da makobcinsu ta shafukan sada zumunta.

Da mijin yake jawabi a gaban kotu cewa yana zargin matan tashi akan cewa sau uku tana tafiya tabar gidanshi, ciki harda wani lokaci da ta bar gidan na tsawon wata biyu ya kuma zarge ta da alaka da makobcinsa wanda take daukan tsawon lokaci tana hira dashi ta internet jaridan aminiya ta rawaito.

Daga karshe kotun da ke zamanta a Ighando a jahan lagos ta raba auren saboda abinda takira da cin amana sakaci da aure da kuma rashin zama tare da matanshi da ya keyi.

Shugaban kotun, Adeniyi Koledeyo, yace raba auren shine zaikawo karshen takaddaman sannan ya umarci mijin da ya biya matan naira dubu 250.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post