Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Ahmed Tinubu, ya ce Nigeriya har ta fara nutsewa, Amma Shugaba Buhari ya tsamo ta,
Ya Kuma ce baya ga nasarorin da shugaban kasa Muhammad ya Buhari ya samu a cikin shekaru bakwai da suka gabata.
Tinubu ya bayyana haka ne a jiya Talata a Jos a wurin ƙaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na 2023.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya bayyana cewa Buhari ya taka rawar gani a fannin samar da ababen more rayuwa tare da kafa ginshikin bunkasa noma da sauran fannoni.
“Ba mu da kwanciyar hankali, sai mu ka koma ga Janar Muhammadu Buhari mai ritaya, ya kuma fara farfadowa da kwato Nijeriya.
“Najeriya ta fara nutsewa amma sai Buhari ya tsamo mu ya kuma ce Nijeriya ba za ta nutse ba a zamaninsa da kuma lokacin APC,” inji Tinubu
Tags:
Dandalin siyasa
