Wani Sojan Najeriya Ya Kashe Abokiyar Aikin Shi Har Lahira.

Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

Wani sojan Najeriya ya kashe ma'aikaciyar Agajin Mata, Ya Raunata Matuƙin jirgin Sama, Da Sauran Ma'aikatan majalisar ɗinkin duniya a Borno.

Wani sojan da ke aiki da runduna ta musamman ta 25 "Task Force" (TF) ta musamman a garin Damboa da ke jihar Borno, an bayyana cewa an kashe shi bayan da ya je daji, inda ya kashe wani farar hula da ba shi da makami, da wani sojan sa, tare da jikkata wasu da dama.

An samu labarin cewa sojan ya buɗe wuta, lamarin da ya yi sanadin kashe akalla mace daya mai aikin agaji da kuma raunata wani matuƙin jirgin na Majalisar Ɗinkin Duniya.

An ce sojan ya fita ne da misalin karfe 3 na yammacin ranar Alhamis inda ya yi harbi da bindiga ta hanyar amfani da bindiga kirar AK-47.

Lamarin da ya tilastawa fasinjojin kungiyoyin sa-kai na ƙasa-da-ƙasa da suke jira su hau jirgi mai saukar ungulu su koma Maiduguri da nufin tsira da rayukansu, kamar yadda wata majiya a Majalisar Ɗinkin Duniya ta shaidawa Zagazola Makama, wani kwararre kan yaki da tada kayar baya kuma mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi.

A cewar rahoton, bayan da sojan ya kare harsashinsa, sai ya fito da wuƙar jiki ya daɓa wa wata ma’aikaciyar kungiyar agaji ta Medecins du Monde (Faransa) ta Najeriya ta mission, inda ya cake ta har sau hudu kafin ya raunata matukin jirgin mai saukar ungulu.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post