Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga
Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 38 da haihuwa bisa zargin kashe surukinshi a yankin Akodo da ke jihar lagos.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, wanda ya bayyana hakan a dandalin sada zumunta, ya ce binciken farko ya nuna wanda ake zargin ya kashe surukinsa ne bayan kamashi yana lalata da ‘yarsu ‘yar shekara 14.
Hundeyin ya ce wanda ake zargin yakuma yaƙara aikata wani laifin inda yakashe wani mutum da ya shaida cewa ya aikata laifin.
Inuwar Labarai
