DA DUMI-DUMI: EFCC ta kwato N30bn daga hannun Akanta Janar Idris Ahmed da aka dakatar


 

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC, a ranar Alhamis, ta ce zuwa yanzu ta kwato sama da Naira biliyan 30 daga cikin ayyukan cin hanci da rashawa da ya dabaibaye babban Akanta Janar na Tarayya (AGF), Idris Ahmed da aka dakatar.

Shugaban Hukumar, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a taron manema labarai da tawagar shugaban ƙasa kan sadarwa ta shirya a fadar shugaban ƙasan da ke Abuja.

Ku tuna cewa a halin yanzu Hukumar tana tuhumar AGF da ke ɗaure a kai bisa zargin almundahanar Naira biliyan 109.

Da yake bayar da karin haske kan nasarorin da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta samu daga watan Janairu zuwa Disamba, 2022, shugaban na EFCC ya bayar da wasu kwato kuɗin sama da N134,33,759,574.25, $121,769,076.30, £21,020.00, €156,925.00, 50.0.00, C50.0,00, da dai sauransu.

Ya kuma bayyana cewa sama da mutane 3,615 aka yanke musu hukunci a cikin wannan lokaci, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin da gaske take kan shirinta na yaƙi da cin hanci da rashawa a wannan ƙasar.

Ya sanar da cewa, za a yi gwanjon motocin da aka yi watsi da su a faɗin ƙasar tare da jefar da gidaje sama da 150 ga masu sha'awar saye.

Bawa ya tabbatar da cewa, a lokacin da hukumar da ke yaƙi da safarar kuɗaɗen haram (SCMUL) ta fara aiki, zai yi wuya a yi amfani da kuɗaɗen haram a kasar nan.

RAHOTO:- COMRADE YUSHA'U GARBA SHANGA

Post a Comment

Previous Post Next Post