DA ƊUMI-ƊUMI: Iran ta rataye mutum huɗu kan zargin yiwa Isra'ila aikin leken Asiri


Ƙasar Iran ta rataye mutum huɗu kan zargin aiki wa Isra'ila


Iran ta rataye mutum huɗu waɗanda ake zargin su da yi wa hukumar leƙen asiri ta Isra’ila aiki.


Kamfanin dillancin labaru na Mizan ya ruwaito cewar an zartar da hukuncin ne a ranar Lahadi.


A Larabar makon jiya ne kotun ƙolin ƙasar ta tabbatar da hukuncin kisan a kan mutanen waɗanda aka kama a cikin watan Mayu.


Haka nan an yanke hukuncin ɗauri na shekara biyar zuwa goma a kan mutane da aka samu da saɓa dokar ƙasa, da garkuwa da mutane da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.


Iran da Isra’ila dai ƙasashe ne biyu waɗanda ba su ga-maciji da juna.


Wannan hukunci ya zo ne yayin da ƙasar ta Iran ke ci gaba da fama da masu boren adawa da gwamnati.

Post a Comment

Previous Post Next Post