Wasu matasa 4 da rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta kama bisa zargin kashe wata mata mai suna Martha Mamman kan zargin maita.
Wadanda ake zargin sun hada da Dogara James mai shekaru 34 da Emma Pious mai shekaru 22 da Irmiya Joshua mai shekaru 22 da Sini James mai shekaru 22 sun fito ne daga unguwar Mugule da ke unguwar Via karamar hukumar Michika.
Da suke ba da labarin mummunar lamarin ga jaridar NEWS PLATFORM a hedikwatar ‘yan sanda a ranar Laraba, wadanda ake zargin sun amince da aikata wannan danyen aikin.
Yayin zantawa , da daya daga cikin wadanda ake zargin, Dogara James, ya bayyana cewa marigayiyar ta amsa laifin cinye mutane 3 a gidan hakimin unguwar.
Ya ce bayan ‘yan kwanaki ne suka kai farmaki gidan marigayiyar inda suka fara lakada mata duka a sakamakon da ta ce ta yi sanadin mutuwar wasu mutane 3.
Ya bayyana cewa yayin da suke lakada mata duka wasu samari sun zo wurin da man fetur da aka yi amfani da shi wajen kona marigayiya Martha.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya ce ana kan binciken wadanda ake zargin.
SP Nguroje, ya ce kwamishinan ‘yan sanda, S. K. Akande, ya bayar da umarnin gurfanar da wadanda ake zargin zuwa kotu bayan bincike, sannan ya gargadi jama’a da su guji daukar doka a hannun su.
Tushe Jarida Radio
Tags:
LABARAN DUNIYA
