"Ta hanyar karance-karance na zamanto marubuci" inji Rufaida Abubakar Adam


Malam Rufai Abubakar Adam, wanda  a rubuce-rubuce aka fi Sani da  R.A Adam, haifaffen garin Gombe ne.Ya kasance fitaccen Marubuci da ya rubuta Littafai masu tarin yawa.

A ɓangaren karatu a yanzu haka ya  kammala degree a  jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi, inda ya karanci koyar da fasahar gine-gine wato Building Technology Education. A wannan Hirar da ya yi da Jaridar "INUWAR LABARAI" ya bayyana yadda ya tsinci kansa a Duniyar rubutu da wasu batutuwa masu yawa da suka Shafi rayuwarsa,ga dai Hirar nan asha karatu lafiya.

R.A ADAM


Ka gabatar da kan ka ga masu karatunmu.

Sunana Rufai Abubakar Adam, amma a rubuce-rubuce an fi sanina da R.A Adam, ni haifaffen garin Gombe ne, a nan na taso na yi karatu kuma a nan nake rayuwa, ni marubuci ne kuma malamin makaranta, mai aikin zane-zane da aikin kumfuta, kuma wanda ya ƙirƙiri shafin Taskar Ƙasar Hausa a yanar gizo.

Wadanne irin marhalolin karatu ka taka zuwa yanzu?

A ɓangaren karatu a yanzu haka na kammala degree a  jami'ar Abubakar Tafawa Ɓalewa da ke Bauchi, inda na karanci koyar da fasahar gine-gine wato Building Technology Education.   Sannan na yi kwasa-kwasa mabanbanta a ɓangaren komfuta da zane-zane, da kuma kwasa-kwasai a fannin malanta.
R.A ADAM


Yaushe ka tsinci kan ka a Duniyar rubutu?

Na tsinci kaina a duniyar rubutu ne tun ina makarantar firamare wajejen 1997 kenan, na taso da ɗabi'ar karance-karance, a lokacin duk kuɗin da nake ɗan samu a sayen littatafai yake ƙarewa, na tara littatafai masu yawan gaske, har ta kai ga ina bayar da hayan su. 

Me ya sa ka tsunduma a fagen rubutu?

Yawan karance-karance ne ya sa na fara rubutu, hakan shi ya buɗe mini ƙwaƙwalwa har na fara rubutu. Na fara rubutu ne a wajejen shekarar 2004 a lokacin ina makarantar sakandire na rubuta wani littafi mai suna Wasa Ƙwaƙwalwa, na kai maɗaba'a domin a buga mini, amma cikin rashin sa'a sai littafin ya ɓata.
R.A ADAM


Zuwa yanzu ka rubuta Littafai guda nawa, sannan wane Littafi ne Bakandamiyarka?

Zuwa yanzu na rubuta littatafai kusan takwas Nafsuzzakiya (2006), Bahaguwar Fahimta (2009), Mathemagics (2016), Ina Son Ki (2017), Lu'ulu'u A Cikin Juji (2022), Duniyar Audu (2022), Sai Farautar Dukiya da wanda na juya shi zuwa fim yanzu haka ana ɗaukar sa. Da kuma na haɗaka guda biyu Dambarwar Siyasa da Siyasa Ba Da Gaba Ba. Sai kuma waɗanda ba a buga ba.

Bakandamiyata a cikinsu shi ne Bahaguwar Fahimta ba don komai ba sai saboda tsawon shekaru da na ɗauka ina rubutawa.


Kowanne marubuci yana da wani marubuci da ya fi burge shi a rayuwarsa wanne marubuci ne ya fi maka tasiri?

Babban marubucin da littatafansa suka fi tasiri a rayuwata shi ne James Hadley Chase, kusan sai da na mallaki dukkanin littatafansa guda casa'in da ya rubuta. A nan gida kuma Dokta Abubakar Imam da Ado Ahmad Gidan Dabino da Nazir Adam Salihi da Shafi'u Dauda Giwa da suna cikin marubutan da nake jin daɗin littatafansu.


Wane kule ka fuskanta dangane da rubutu?

Alhamdulillahi, zan iya cewa ban wani fuskantar ƙalubale ba a rubuce-rubucen da nake yi, hakan yan da nasaba ne da yadda Allah ya azurtani da jajirtaccen uba mai son ganin 'ya'yansa sun yi karatu, kullum yakan ƙarfafe ni da na yi karatu wanda hakan shi ya taimake ni har na zama marubuci.

Wadanne nasarori za ka iya bayyanawa na rubutu?

Alhamdulillahi, babban nasarar da na samu a rubutu sun haɗa da yadda nake amfani da rubutu wajrn isar da saƙo mai kyau a cikin al'umma, yawancin littatafan da nake rubutawa ba haka kawai na rubuta su ba ko don neman kuɗi ko sha'awa ba, ina rubutu ne don isar da wani muhimmin saƙo a kan wata matsala da ta dami al'umma. 

Sannan na taɓa zama ɗaya daga cikin marubuta 15 da labaransu suka yi zarra cikin marubuta kusan 250 a gasar Aminiya Trust da aka yi 2020 mai taken Dambarwar Siyasa. 



Da gaske marubuci zai iya amfani da  social media wajen isar sa sakon shi ga al'umma?

Ƙwarai ma kuwa, domin kusan yanzu ta nan muke tallata littatafan da muka wallafa, mu kuma sayar da su ta hanyar PDF duka ta social media. 

Sannan ta social media ne muke sada zumunci a tsakaninmu, wanda har hakan ya bamu daman haɗa kan mafi yawancin marubuta da ke Gombe a wani zaurenmu mai suna Taskar Ƙasar Hausa, ana gabatar da darussa a kan abin da ya shafi adabi da ƙa'idojin rubutu a zauren, kusan duk a nan ma muka koyi ƙa'idojin rubutun Hausa. Wanda hakan ya kai ga mun samar da shafin a yanar gizo mai adireshi kamar haka taskarkasarhausa.blogspot.com inda muke ɗaura littatafai mabanbanta da maƙaloli kala-kala, duk a dalilin soshiyal midiya.

Me za ka ce ga marubuta masu tasowa?

 Mu rubuta abu mai kyau kuma mai amfani, domin ta hakan ne ko bayan ba ranka za ake tunawa da kai kamar yadda ake tunawa da su Dokta Abubakar Imam, da su Ahmadu Ingawa da su Abdullahi Mukhtar Yaron Malam da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post