Wata mata mai matsakaitan shekaru ta yanke jiki ta fadi ta mutu bayan da aka kai mata tallafin kudi sama da naira dubu dari da sittin domin a hadawa babbar yarta kayan aure dakin miji,
Tun bayan rasuwar mahaifinsu, matar ita ce ta ke rike da yaran su bakwai wanda sai ta je aikatau a gidan masu hali sannan take samun abinda za ta ba su.
Matar dai da yaran na ta dukkaninsu mazauna jihar Bauchi ne,
Shahararriyar marubuciyar nan kuma Mai gidauniyyar tallafawa marayu da marasa galihu wato Needy helpy Faundation Fauziyya D. Sulaiman ita ce ta bayyana haka a wani Video da ta turawa manema labarai,
Inda ta ce wannan kungiyar ta tura wakilci zuwa Bauchi a ranar Alhamis domin akai tallafin kudi da za’a yiwa yarinyar hidimar aure.
"Bayan mun baiwa mahaifiyar yarinyar kudin ne ta fara kuka tana godiya har ta durkusa kasa tana godiya ga Allah (Sujada Shukr) tana cewa ashe za taga auran yarta ? Ashe wannan lokacin zaizo tana da rai ? Daga nan bata sake motsi ba rai ya yi halinsa". Ta bakin Fauziyya D. Sulaiman
Ta kara da cewa dole za’a daga lokacin daurin auran wanda da aka niyyar yin auren jiya Asabar amma babban kalubalen shi ne ragowar yara shida da ta bari marayu yadda rayuwar su za ta kasance.
Tags:
Abun Al'ajabi

