A ranar Bakwai ga watan Janairu, Shekarar Alif da Ɗari Takwas da Casa’in da Bakwai (1897), Lady Flora Shaw, uwar gidan Lord Lugard wacce ƴar Jarida ce ta fito a karon farko a cikin jaridar Birtaniya, The Times, London da cewa ta ƙirƙiri sunan ƙasar da suke wa Mulkin Mallaka "Nigeria."
Daga baya Lord Lugard, ya haɗe arewa da kudanci a ranar Ɗaya ga watan Janairun Alif da Ɗari Tara da Goma Sha Huɗu (1914), saboda dalilai na tattalin arziki kawai.
Gwamnatin turawan mulkin mallaka ta Ingila ta yi musu su na da sunan Najeriya a farkon shekarar Alif da Ɗari Tara (1900).
An ciro sunan Najeriya ne daga kogin Neja da ya ratsa ƙasar. An kuma ƙirƙiro wannan suna ne a ranar Bakwai ga Watan Janairu, Alif da Ɗari Takwas da Casa’in da Bakwai (1897), daga wata ƴar jarida ta Burtaniya Flora Shaw, wacce daga baya ta auri Lord Lugard, wani mai kula da mulkin mallaka na Burtaniya.
Kafin lokacin tsohon sunan Najeriya shi ne; Royal Niger Company (RNC).
Taskar Nasaba
Tags:
DANDALIN TARIHI
