Wata mata ta haihu a masallacin Annabi (S.A.W) dake birnin Madina


 Wata mata cikin masu gudanar da umra ta haihu a masallacin ma’aiki dake Madinah wacce ta samu taimakon wasu daga cikin masu yima masallacin ma’aiki Sallallahu alaihi Wasallam hidima.


Daraktan kula da masu yima masallatai hidima na ƙasar ta Saudiyya Dakta Ahmed bin Ali Al-Zahrani, yace wasu daga cikin mutanen su dake aikin hidima wa masallacin ne suka taimaka ma matar wajen haihuwar bayan da suka lura da halin da take ciki na naƙuda.


Yace ana cikin gudanar da ibadah ne wasu daga cikin mutanen nasu suka fahimci cewa matar ta na cikin matsanancin hali na naƙuda ta yanda ba zai yiwu ace an kaita asibiti ba, kamar yadda majiyar mu ta wallafa.


Ya kuma ƙara da cewa daga nan ne mutanen nasu suka bazama cikin aikin agajin gaggawa tare da haɗin gwuiwar wasu masana lafiya a gurin waɗanda suka taimaka mata ta haihu lafiya tare da cika duk wasu sharuɗɗan aikin lafiya.


Bayan haihuwar ne kuma aka garzaya da matar da kuma jinjirin nata zuwa wani asibiti dake kusa da gurin domin ƙara tabbatar da lafiyar ta da kuma ta abinda ta haifa, sabili da akwai buƙatar duba lafiyar tata.


Al-Zahrani ya kuma ƙara da cewa dama daga cikin mutanen nasu akwai waɗanda suka ƙware wajen gudanar da irin waɗannan ayyukan wanda a haka suka samu nasarar taimaka matar ta haihu.


Daga ƙarshe Al-Zahrani ya bayar da 997 a matsayin lambar da za’a riƙa amfani da ita wajen kiran gaggawa domin kiran motar agajin gaggawa, wanda hakan zai sauƙaƙa ma ma’aikatan wajen iya gano inda mai kiran yake da sauri.

Post a Comment

Previous Post Next Post