Ya kamata mu hadu mu yi Fim din da zai fitar da mu kunya a daina raina mu--Ado Ahmad Gidandabino

Shahararen jarumi, furodusa, marubuci, Kuma Shugaban Hadadiyar Kungiyar kwararru ta masu shirya Finafinan Hausa reshen jihar Kano MOPPAN Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya yi kira da yan masana'atar Kannywood da a yi haÉ—in gwiwa na kamfanoni da za su haÉ—u su yi babban fim wanda zai fitar da Kannywood kunya, a daina raina mu, 

Inda ya jaddada cewa mu na da labarai masu yawa da ingancin da za mu iya nuna shi a duniya.
Gidan Dabino ya bayyana Hakan ne bayan ya dawo daga taron karramawar gasar wanda aka yi a Abuja ran Asabar da ta gabata inda ya doke mutum 12 da su ka shiga gasar daga ko’ina a Nijeriya.

Nasarar da ya samu kwanan nan ta zama na É—aya a wata gasa ta Æ™asa baki É—aya mai suna ‘Nigerian Most Respected CEOs Awards’,  
Gwamnan na Alfawa ya ce: “To, ita wannan gasa dai ana kiran ta da ‘Nigerian Most Respected CEOs Awards’. Kuma ana zaÉ“ar mutane ne ta hanyar ‘online’ a ce a jefa musu Æ™uri’a. Kuma ina cikin mutane goma sha uku waÉ—anda aka zaÉ“o a cikin masu harkar fim. Kuma dukkan su ma daga kudancin Nijeriya su ke, ni kaÉ—ai ne É—an Kannywood.

“Saboda haka da aka jefa Æ™uri’a, ni na samu mafi rinjaye, wadda hakan ta sa aka ba ni kyauta a matsayin wanda ya yi nasara a gasar.

“Kuma ka gane, a kowane matsayi ana zaÉ“ar mutum É—aya da ya yi nasara ne, don ba a kan fim kaÉ—ai aka yi ba. An yi a kan noma, an yi a kan injiniya, an yi a kan Æ™irÆ™ira da kwalliya. Haka dai abin ya kasance, maza da mata.
“Kowane É“angare na sana’a mutum É—aya ake zaÉ“a. Amma dai ina ganin mu a É“angaren fim, mu mu ka fi kowa yawa da har mu ka kai mu goma sha uku, don a sauran duk babu waÉ—anda su ka kai haka a cikin waÉ—anda su ka shiga gasar.”
Da mu ka tambaye shi ko me ya bambanta wannan karramawar da sauran waÉ—anda aka saba yi masa a baya kuwa, cewa ya yi: “To, abin da ya bambanta su shi ne su waÉ—anda su ka shirya wannan gasa ba su san ni ba, ban san su ba. Kuma ni ban ma taÉ“a jin labarin su ba, sai daga lokacin da na ga an sako hotunan mu mu goma sha uku kuma an tura aka ce mutane su jefa musu Æ™uri’a.

“Kuma su asali su na da ofishin su ne a Legas, su na da shi a Abuja da Ghana, don haka su na shirya taron ne a duk in da ofishin su ya ke.

 ce: “Abin da zan faÉ—a, mutane, musamman ‘yan fim na Kannywood, su sani wannan gasa da na samu nasara ba nasara ta ce ni kaÉ—ai ba, ta masana’antar finafinai ta Kannywood ce duka, domin kuwa akwai jarumai da furodusoshi da daraktoci da su ka zo daga Kudu, amma ni kaÉ—ai aka zaÉ“a daga Arewa kuma É—an Kannywood da ake ganin an fi mu iyawa. Don haka mutane su É—auki wannan gasa tasu ce. Don kuwa bayan gasar na je da fim É—in ‘Juyin Sarauta’ an haska shi a wajen, kuma abin ya burge su, su na ganin fim É—in ya bambanta da waÉ—anda su ka saba gani na Kannywood na rawa da waÆ™a, don haka sun yaba da aikin. 

“To, ka ga za mu iya yi idan mun dage, kuma za mu iya yin takara da waÉ—anda su ke ganin sun sha gaban mu" a cewar Gidandabino

Post a Comment

Previous Post Next Post