YOBE: Mai Mala Buni ya kafa kwamitin kame masu cin zarafin kananan yara da Matan aure


Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni, ya Kaddamar da kwamitin yaki da Cin zarafin Mata da Kananar Yara, Kwamitin da zaiyi aiki na Tsawon Kwanaki 16 a karamar Hukumar Damaturu dake a Jihar Yoben.

  

Acewar Gwamnan Kwanaki 16 da za'ayi ana aiki Zasu Kasance na Tattaki ne a kwanakin duniya da aka ware Domin yaki da cin zarafin mata da Kananar yara.   

  

Gwamna Buni Wanda ya samu Wakilcin mataimakinsa Alh. Idi Gubana yace, Za'a Fara Tattakin ne da Safiyar litinin din da ya gabata. Kamar yadda Majalisar Dunkin Duniya Ta Ware Ranakun Musamman Domin Yaki da cin zarafin mata da ƙananar Yara.

 

Kuma da Babban Murya Cikin Amon da ba'a rasaba Ganin masu mulki nayi Ba, Mataimakin Gwaamnan Yace, Daga Wannan rana Har Zuwa Ranar da za'a kammala Tattakin Gwamnaati Zata bada abunda ake bukata, kama Daga kan Tallafi da Kuma Wasu abubuwan da za'ayi amfani Zasu a Yayin Tattakin.


Anata Jawabin Kwamishiniyar Mata Hajiya Hawwa Bawa Abubakar ta bayyana jin Dadinta daya Yadda Jihar tabi sauran jihohi wurin yin Tattakin,Ta kuma nuna farin Cikinta kan yadda taron Yasamu halartar Mutane da Dama,Ta kuma CE daga cikin abubuwan da sukeson cimmawa a karshen wannan Shekaran shine hada hannu wuri guda domin Zama Tsintsiya madaurinki daya wurin shawo kan matasalar tare da Cimma abunda akeson cimmawa.

 

Haka Kuma Ta Bukaci yan Jarida, jamian tsaro, 'yan siyasa da lauyoyi da masu sharia dasu kasan ce masu bada Gudummawar da ake bukata, Domin sune jigo na dukkanin gyaruwar wata al'umma.


Tattakin da ake fatar ya Haifar da da mai ido zai dunga Gudana ne tareda wayar da kan Al'umma kan illar dake tattare da cin zarafin mata da Kananar yara, Taken Taron Kwanakin na shekarar 2022 shine, kawo karshen cin Zarafin mata da kananar yara a duniyar baki daya.


Rahoto: Hasana Magaji Kwantagora.

Post a Comment

Previous Post Next Post