![]() |
| Source details from Police |
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta yi holin wasu matasa su 61 da ta cafke bisa zargin su da ayyukan ta’addanci ta hanyar ƙwacen wayoyin mutane a ranar Larabar makon nan.
Rundunar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ta SP Abdullahi Haruna, ya fitar a daren Alhamis ɗin nan.
Kazalika, sanarwar ta ce, an cafke matasan ne ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi yayin gudanarda taron bada tutar ƴan takarar jam’iyyar APC a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
