Duk masu sukar Gwamnatin shugaba Buhari dakikai ne -- inji Lai muhammad



Ministan yada labarai da al’adu na kasa, Lai Mohammed ya caccaki masu sukar Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan lalacewar tattalin arziki, inda ya bayyana su da cewa Dakikai ne.


Ya bayyana hakan ne  yayin da yake jawabi a taron bayyana nasaorin Antoni Janar na kasa kuma ministan shari’a, Abubakar Malami, Lai Mohammed ya bayyana cewa Gwamnati tayi matukar kokari a shekaru 8 da suka gabata kuma jam’iyyarsu ta cancanci a sake bata dama.



Ya Kara da cewa “Gwamnatin Buhari a shirye take ta kara shayar da ‘yan Nijeriya roman dimukuradiyya,  Kamar yadda kuka sani, an kammala aikin nan na gadar Niger ta 2 kuma za a bude shi nan bada jimawa ba.”


Bayan zayya no wasu ayyukan da Gwamnatin Buhari ta aiwatar, Lai Mohammed ya ce aikin jahilci ne masu sukar gwamnatin shugaban kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post