KIWON LAFIYA: Kwamitin Bincike ya Gano Likitocin Bogi Sama Da 130 a Kano

Wani kwamiti da karamar hukumar Tudun Wada ta jihar Kano ya fitar ya bayyana cewa ya gano asibitoci da shagunan sayar da magunguna 130 da likitocin bogi ke tafiyar da su.

Kwamitin wadda shugaban karamar hukumar, Alhaji Tijjani Matata, ya kafa ya ce, yayin bincikensa ya gano daya cikin likitocin injiniya ne na lantarki wanda ke da asibiti mai gado takwas da ya yi ikirarin yana maganin kowane ciwo.

Matata ya bayyanawa manema labarai cewa, daya daga cikin likitocin bogin ya saka wa wata mata jini mai cutar kanjamau lokacin da ta zo yin maganin zazabin cizon sauro.
Ya kara da cewar: “Abin takaici ne yadda mu ka gano injiniya na lantarki yana tafiyar da asibiti mai zaman kansa, yana ganin marasa lafiya yana rubuta magani da karin ruwa da kuma jini, har yana kulawa da masu ciki! Daya daga cikinsu har wata mata mai ciki ya sakawa HIV.

Mun gano wani mai maganin gargajiya, amma yana kwantar da masu kwalara.

Mun kwashe su mun kai su asibiti.

INCREASE IN FEES BY PUBLIC UNIVERSITIES: WHY COMPLAIN?

 Read more 👇👇


Mafi yawancin su ba su san komai game da kiwon lafiya ba.

Matata ya kara da cewa “Daya daga cikinsu ya ce shi malamin jinya ne amma muka gano satifiket din sakandare kawai gare shi.

"Kuma munyi binciken ne bayan korafe-korafe da dama da muka samu daga mazauna yankin kan karuwar asibitoci masu zaman kansu da shagunan magani a kauyukansu. In Ji shi"

Post a Comment

Previous Post Next Post