![]() |
| Details from INEC |
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ce ta yi wa mutane Milyan 93, 469,008 rajista a zaben 2023.
Rahotanni sun ce cikin adadin mutane sama da mutane milyan 93, maza suna da kashi 52.5 yayin da mata ke da kashi 47.5 na jimillar adadin.
Jerin sunayen masu rajista na karshe da hukumar zabe ta fitar a ranar Laraba ga jam’iyyun siyasa a hedikwatar hukumar da ke Abuja, ya tabbatar da wannan kididdiga.
Rahoton ya cigaba da cewa Legas ce ke kan gaba da masu rajistar zabe Milyan 7,060,195 yayin da jihar Kano ke da 5,921,370.
A yanzu haka dai ana saran zuwa ranar 25 ga watan Fabrairu wata mai kamawa ne ‘yan Najeriya za su fita filin daga domin zabar shugabanni a matakai daban daban
