Ƴar takarar gwamnan jihar Kano a Jam’iyyar NRM Hajiya Aishatu Mahmoud ta bayyana cewa gazawar da Maza su ka yi wajen magance matsalolin Kano da samar da ingantacciyar rayuwa ne ya sanya ta fito takarar gwamna.
Aishatu Mahmoud ta bayyana hakan ne a yau Lahadi a gurin taron tattaunawa da yan takarar gwamnan Kano da cibiyar nazarin harkokin demokardiyya da bayar da horo ta Malam Aminu Kano ta shirya.
“Gazawar Maza ce ta sanya na fito takarar neman kujerar gwamnan jihar Kano”
Kazalika ƴar takarar gwamnan ta soki maganar da yan siyasa su ke yi kan bayar da ilimi kyau a jihar Kano, inda ta bayyana tsarin a matsayin yaudara da wasa da hankali.
“Ilimi kyauta yaudarar kai ne. Sassaucin rayuwa ta hanyar bayar da tallafi a bangaren ilimi shi ne mafita”
Sannan daga karshe Aishatu Mahmoud ta ce Idan ta yi nasarar lashe zabe gwamnatin ta za ta dauki nauyin karatun marayu daga matakin firamare zuwa Jami’a tare kuma da bayar da tallafi yin sana’a ga masu bukata ta musamman.
