Rikicin jagoranci ya tilasta rashin yin sallar Jumu'a a Masallacin Darul Hadith na marigayi Dr. Ahmad Ibrahim BUK, a jiya Juma'a,
Tarzoma ta kaure a Masallacin ne lokacin da sabon liman zai hau Mumbari don soma huɗu ba, inda wasu fusatattu suka janyo rigarsa ta baya don nuna ƙin amincewa da shi, lamarin da ya kawo rikici.
Tuni aka rufe masallacin tare da baza jami'an tsaro a kofa da kewayensa.
Yanzu haka dai tuni ɓangarorin biyu suka nufi shalkwatar ƴan sanda da ke Bompai domin sasantawa.
Rahotanni da muka samu sun nuna cewa, wasu mutane ne da ba su Fi mutum biyar ba ne, suka zo da wani sabon liman, inda ya wuce gaba zai gudanar da sallah ya yin da su Kuma alumma suka ga ba su sanshi ba suka jawo shi.
