Zan Rushe duk wani Gini da Aka yi a jikin Badala Idan na Zama Gwamnan Kano – Dawisu.

Dawisun Kano

Dan takarar Gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PRP, Salihu Tanko Yakasai da aka sani da Dawisu, ya bayyana cewa idan ya samu damar zama Gwamnan jihar Kano zai rushe duk gine ginen da aka yi a jikin Badala a jihar.

Salihu Tanko Yakasai ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi a muhawarar ‘yan takarar Gwamna da ya gudana a jiya Lahadi a gidan Munbayya dake Kano.

Taron wanda jami’ar Bayero da hadin gwiwa da wasu kungiyoyi masu kansu suka shirya ya samu halarta kusan mafi yawan ƴan takara na Jam'iyu daban-daban a Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post