CIKIN HOTUNA: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Bayyana Sanata Aliero Da Dr Yahaya Matsayin 'Yantakara


Daga Comrade Yusha'u Garba Shanga. 


A ranar 30/01/2023 kotun ɗaukaka ƙara dake zamanta kanta a babban birnin tarayya, Abuja ta tabbatar da takarar Sanata Muhammadu Adamu Aliero da kuma sanata Dakta Yahayya Abdullahi Mallamawan Kabi.


Biyo bayan ƙarar da abokan karawar ‘yan takarar masu neman sanata suka shigar ƙarkashin jam’iyyar adawa ta PDP a watannin da suka gabata.


Abokan karawar ‘yan takarar na zargin Sanata Adamu Aliero da kuma Mallamawan kabi da kwacen tikitin tsayawa takara bayan gudanar da zaɓen fidda gwani a takara watannin da suka gabata.


Hakan ya tunzurasu da shigar da kara inda aka fara gudanar da shari’a a babbar kotun tarayya dake jihar Kebbi. 


Inda kotun ta bayyana malam Haruna a matsayin shine halastattacen ɗan takara ba sanata Adamu da malamawa ba. 


Bayan rashin gamsuwar hakan Suka garzaya a kotun Ɗaukaka ƙara dake jihar Sokoto, inda kuma aka sake zaman kotu, jim kaɗan kotun ta ƙara bayyana su malam Haruna a matsayin masu nasara tare da yin watsi da ƙarar sanata Aliero. 


Inda Shi Sanata Yahaya ya bayyanawa 'Yan jam' iyyar PDP cewa yabarwa Allah, sai dai shuwagaban jam'iyyar na jiha Usman Bello Suru yaɗau hakan amatsayin ƙanzon kurege, tare da cewa zasu Ɗaukaka ƙara izuwa kotun ƙoli... 


Haka zalika sanata Adamu Muhammad Aliero Shima ya ja daddawa magoya bayanshi da suyi haƙuri insha Allah zasu Ɗaukaka ƙara izuwa kotun ƙoli. 


Hukuncin kotun Sokoto ya kasa gamsar da ‘yan takarkarun hakan yasa suka Ɗaukaka ƙara zuwa kotun daukaka kara dake babban birnin tarayya Abuja.


Malam Haruna wanda shine abokin karawar sanata Adamu Aliero a takarar sanatan Kebbi ta tsakiya a ƙarkashin jam’iyyar adawa ta PDP yayi rashin nasara bayan ya ɗaukaka kara akan Aliero.


Yau dai ankai ƙarshen zaman kotun inda ta bayyana cewa Sanata Adamu Aliero shine halastattacen ɗan takarar sanatan Kebbi ta tsakiya a jam'iyyar PDP. 


Haka zalika Sanata Dr Yahaya Abdullahi Malamawan Kabi shine halastattacen ɗan takarar sanatan Kebbi ta Arewa.






 

Post a Comment

Previous Post Next Post