KANYWOOD:Jarumi Ali Nuhu ya janye karar da ya kai Hannatu Bashir a gaban kotu

Daga Ibrahim Hamisu

Fitaccen jarumin finafinan Hausa na Kannywood Ali Nuhu ya janye karar da ya kai Jaruma Hannanu Bashir na cin zarafi da ya ce ta yi.

Tun da farko dai takaddama ta taso ne a tsanin jaruman biyu bayan Ali Nuhu ya gaza halartar wurin daukar Fim din da Hannanu Bashir din ta shirya, lamarin da ya bata mata rai har ta tura masa maganganu. In da shi kuma ya maka ta a gaban kotun. 

A zaman kotun da Hannatu Bashir ta halatta, lauyar Ali Nuhu ta bayyana wa kotun cewa wanda ta ke wakilta ya janye karar da take wakilta, biyo bayan sulhun da ake kokarin yi a tsakanin jaruman biyu.
Sai dai jarumar ba ta ji dadin abinda lauyar Ali Nuhu ta fada mata ba, inda ta ce " Bansan me ya sa za ta je gidan radio ta dinga wasu surotai ba, wai na je ina ta kiran manyan mutane da manyan yan Kannywood Ina ce musu wai su ba shi hakuri ba, ban san me yasa ta fada ba watakila don ta gyara aikinta ne ko ta ji dadin bakinta". A cewar Hannatu Bashir

Idan dai zaa iya tunanawa a makon jiya ne Jarumi Ali Nuhu ya maka Hannatu Bashir a gaban kotun majistry da ke zamanta a noman sland da ke jihar Kano, inda ya zargeta da cin zarafinsa. A yanzu dai alkali ya sulhunta su ya ce suke su cigaba da aikinsu cikin lumana da kwanciyar hankali.

Post a Comment

Previous Post Next Post