SIYASA: Tinubu ya mika Tallafin naira Miliyan 100 a Kano~Daga Ibrahim Hamisu

Zuwan Tinubu kano
Mai yiwa jam'iyyar APC takararar Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da gudunmawar Naira miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Kano.

Tinubu wanda ya kawo ziyarar kwanaki 2 a Kano, ya bayar da gudunmawar ne a lokacin liyafar cin abinci da kungiyar ‘yan kasuwa ta Kano ta shirya masa domin karrama shi.
Zuwan Tinubu kano

Ya ce sun bayar da tallafin ne domin taimakawa da rage radadin ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kananan hukumomin da abin ya shafa.

Rahotanni sun nuna cewa an samu ambaliyar ruwa a kananan hukumomi 19 cikin 44 na jihar Kano, inda mutane 23 suka mutu, 106 suka jikkata, sannan gidaje 12,919 suka lalace yayin da gonaki 14, 496 suka lalace a kananan hukumomin biyar.
Zuwan Tinubu kano 

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya yi alkawarin sake mayar da masana’antun da ake da su tare da mayar da su a matsayin tushen ci gaban masana’antu da bunkasa ba kawai ga Arewa ko Kano ba har ma da kasa baki daya.

Haka kuma ya yabawa Gwamna Abdullahi Ganduje bisa kokarinsa na samar da ababen more rayuwa a jihar, inda ya bayyana gwamnan a matsayin “aboki kuma amintaccen abokin tarayya”.

Sannan ya yi wa ’yan kasuwar alkawarin cewa zai samar da yanayin da zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwanci a jihar.

Su ma ‘yan kasuwar sun gabatar da tsarinsu ga Tinubu, inda suka yi kira gare shi da ya mai da hankali kan wutar lantarki saboda an rufe masana’antu da yawa saboda rashin isasshen wutar lantarki.

Post a Comment

Previous Post Next Post