"Ko wanne da Nigeria ya Kare kansa gwamnati bazata iya Kare ku ba" ~Inji TY Danjuma

TY Danjuma
Tsohon Ministan Tsaro, Theophilus Danjuma, ya sake yin kira ga ƴan Nijeriya da su ɗauki makamai su kare kansu daga ƴan ta’adda da ƴan fashin jeji.

Janar din sojan mai ritaya ya yi wannan kiran ne a wajen bikin bada sandar sarauta ga Aku-Uka na Wukari a Jihar Taraba, Manu Ishaku Adda Ali, a yau Asabar.

Danjuma, wanda irin wannan kiran da ya yi a shekarar 2018 ya janyo cecekuce a ƙasa, ya yi zargin cewa kasar na fuskantar mamaya daga ƴan ta’addan kasashen waje da ke karɓe filayen jama’a.

“A matsayina na soja, mafi kyawun tsaron kai shine kai hari. A yanzu, duk muna zaune agwagi. Wadannan mutane suna dauke da makamai har na ƙare-dangi, amma mu ba mu da su.

“Mu na da yawa kuma ƙasarmu ce. Su na kokarin su yi mana mulkin mallaka ne su kwace mana filayenmu. Ranka ya dade, dole ne ka hada kan jama’ar mu don kare kansu,” inji shi.

Yayin da yake kira ga jama’a da su gano inda ‘yan ta’addan ke samun makamai domin ta’addanci kan ƴan kasa da ba su ji ba ba su gani ba, Danjuma ya ce ba zai baiwa kowa makami ba.

“Ba zan ba ku makamai ba. Ku gano yadda mutanen da suke da shi suka same shi kuma ku yi amfani da wannan hanyar don samun makamai ku kare kanku."

© Daily Nigerian Hausa 

Post a Comment

Previous Post Next Post