Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga
Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya dage cewa shi da magoya bayansa ba su sauya ra’ayi ba game da ƙin goyon bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, na Atiku Abubakar.
Wike ya dage da cewa sai dai Iyorchia Ayu ya ajiye muƙaminsa na Shugaban PDP na ƙasa kuma ya maye gurbinsa da ɗan kudu, Atiku da jam’iyyar su kadai ne game da zaɓen shugaban kasa na 2023.
Gwamnan Ribas ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a yayin ƙaddamar da gadar sama a Rumueprikon, ƙaramar hukumar Obio-Akpor a Fatakwal, jihar Ribas wanda tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Adams Oshiomhole ya yi. .
A cewarsa, buƙatarsu ta shafi kiyaye ƙa’idojin daidaito adalci da gaskiya, inda ya ƙara da cewa ba za a yi sulhu ba sai an biya buƙatarsu.
Wike ya kara da cewa wasu na iya ganinsa a matsayin maƙiyin jam'iyyar PDP amma ba haka lamarin yake ba domin yana fafutukar neman gaskiya ne kawai.
Ya ce: “Mutane za su yabe ka amma ranar da ka ce a’a za su yi adawa da kai. Na tabbata waɗanda suke cikin jam’iyyata kafin su iya cewa komai ba tare da sun ambaci Wike ba. Amma yanzu don na ce a yi abin da ya dace, yanzu na zama maƙiyi. Waɗannan mutane ne da suke yabona akan komai.
“Kuma wasu mutane sun yi imanin ba za su yi biyayya ga yarjejeniya ba amma mun ce dole ne a yi. Mun tsaya kan adalci, gaskiya da adalci. Abin da G5 zai ci gaba da wa'azi ke nan. Mun ce ba ma adawa da sulhu amma dole ne a yi adalci a kan gaskiya da adalci”.
