Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
Masu fafutukar kare hakkin jama'a sun hada kai da babbar majalisar matasan kabilar Yarabawa domin nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressive Congress (APC), Bola tinubu.
sun yi taro a sakatariyar jam'iyyar APC ta jihar Oyo a ibadan domin kaddamar da wani yunkuri, hadakar hadin gwiwa don inganta nigeria.
Sunyi amfani da wannan dama wajen ba da lambar yabo ta ‘Africa man of the century odu’a award’ ga Asiwaju Tinubu.
Haka kuma taron ya samu goyon bayan babajide sanwo-olu, Dapo Abiodun da Sanata Teslim Folarin, ’yan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihohin lagos, Ogun da Oyo.
An sanar da kyautar gwarzon dan Afirka a watan Satumban da ya gabata a wani bikin murnar zagayowar ranar Yarabawa.
Shugaban babbar majalisar matasan kabilar Yarabawa, Awa Bamiji, ya bayyana tinubu a matsayin daya daga cikin jiga-jigan dimokuradiyya, ya kara da cewa ana shirye-shiryen wani taron a watan Fabrairu.
Ya ce: “Muna farin cikin karrama daya daga cikin manyan ginshikan dimokuradiyya, mai gina mutane, shugaba tinubu a wannan karo.
"Mun hada karfi da karfe tare da sauran kungiyoyi a duk fadin duniya, karkashin ingantacciyar kungiyar hadin gwiwa don samar da ingantacciyar nigeria, mai gabatar da takarar tinubu a zaben shugaban kasa na 2023.
Bamiji ya yi nuni da wani shiri na ba da tinubu lambar yabo ta babban kwamandan siyasar Afirka da kuma wani mutum-mutumi mai kyau na tinubu yana buga wasan kwallon kafa a matsayin kyaftin din tawagar kwallon kafar Afirka a fagen siyasa.
Wadannan, in ji shi, an shirya su “domin nuna godiya ga gudummawar da tinubu ya bayar wajen bunkasa karfin dan Adam, siyasa, da kasuwanci a Afirka. “
Fitattun shugabanni a ciki da wajen Najeriya sun nuna sha’awar wannan aikin .
"'yan Najeriya mazauna kasashen waje suna fatan haduwa da abokan aikinsu a nan Najeriya", in ji Awa.
Inuwar Labarai RPT 001
Tags:
Dandalin siyasa
