Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)
Allah ya yi wa shaharerren dan jarida mai sharhi kan lamuran yau da kullum a manyan gidajen rediyon duniya Malam Bashir Mohammad Baba rasuwa. Za a gudanar da jana'izar sa a mahaifarsa Wudil a Jihar Kano anjima.
Marigayin ya rasu bayan kwantawa jinya a asibitin taraiya da ke Abuja.
Tabbas mun yi babban rashi. Allah ya jikansa da rahama. Duk da tsananin jinya da ya yi fama da ita ya kan yi kokari ya miko hannu a yi musabaha da shi ya na murmushi ashe bankwana ya ke yi.
