Gwamnatin tarayya ta dawo da darasin Tarihi a Makarantun Nigeriya



Gwamnatin Tarayya ta dawo da darasin tarihi a makarantun FIFA are da sakandare bayan shekara 13 da sokewa.


Ya zuwa yanzu dai gwamnatin ta dauki malaman bangaren na tarihi guda 3,700 domin ba su horo da nufin inganta koyar da darasin a shekarar 2009/20210.


Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimi a Matakin Farko (UBEC), Hamid ya ce an dauki malaman ne a jihohi 36 da Birnin Tarayya, inda a kowace jiha aka dauki mutum 100.


Da yake jawabi a taron kaddamar dawo da darasin da kuma horas da malaman, Ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya ce dakatar da darasin da aka yi a baya ya haifar da karuwar lalacewar tarbiyya da raya al’adu.


Adamu Adamu, ya bayyana haka ne ta bakin Minista a Ma’aikatar Ilimi, Goodluck Opiah, a taron, wanda ya wakilce shi a taron da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar da sauran masu ruwa da tsaki suka halarta.


A jawabinsa, Sarkin Musulmi ya yi kira ga sarakunan gargajiya da sauran ’yan Nijeriya da su taimaka tare da goyon bayan gwamnatin kan dawo da darasin tarihi tun daga makarantun firamare da Kuma sakandare.

Post a Comment

Previous Post Next Post