An Ceto Matan Da Mijinta Ya Daure Ta Na Tsawon Watanni Cikin Wahala A Jihar Yobe.

Daga Abdulnasir Yusuf Ladan

An ceto wata matan aure mai suna Sadiya Haruna mai shekaru 33 a duniya, inda yanzu haka take cikin wani mawuyacin hali bayan mijinta ya daure ta na tsawon watanni a cikin azaba.

Sadiya matan wani dan kasuwa ne a karaman hukuman Nguru da ke jahan yobe, mai suna Ibrahim yunusa Bature, inda ya daure matanshi na tsawon watanni babu dalili har zuwa wasu watanni a cikin mawuyacin hali.

Jaridan Aminiya tayi hira da mahaifiyan Sadiya mai suna Hadiza Hassan, inda ta shaida cewa takai ma 'yarta ziyaran bazata ne sai tayi kacibis da ita a daure cikin wani mawuyacin hali, da azzakumin mijin nata ya sakata a ciki. Inda tace ana zargin mijin nata da yin tsafi da ita daga karshe kuma ya hanata abinci saboda ta mutu.

Hadiza tace, yanzu haka 'yar tata tana kwance asibitin kudi da ke unguwan sheka ta gabas a karaman hukuman Kumbotso da ke jihan Kano.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post