Labarin da ke ishe Inuwar Labarai sun bayyana cewa ƴan sanda sun kama Ambasada Yusuf Imam, wanda a ka fi sani da Ogan Boye, wanda ya ke ƙusa a jam'iyyar adawa ta NNPP a jihar Kano.
Jaridar Sahelian Times, ta ruwaito an kama Ogan Boye ne tun a daren jiya Lahadi a gidansa da ke Ƙaramar hukumar Nassarawa, inda su ka kai shi shelkwatar rundunar.
Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin da ya sa a ka kama Ogan Boye ba, amma kuma Sahelian Times ta ce ba ya rasa nasaba da rigingimun siyasa da su ka fara kunno kai tsakanin APC da NNPP a jihar.
Ya zuwa yanzu dai Muna dakon jin ta bakin hukumar yansanda don Jin Ina aka kwana.
