Wuta Ta Kone Layin Kano a Babbar Kasuwar Onitsha.

Daga Abdulnasir Y. Ladan (Sarki Dan Hausa)

Wani sashe na babbar kasuwa a garin Onitsha na jihar Anambra na fuskantar ibtila'in gobara. Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar da aka ce ta tashi da tsakar dare ba.

Wani dan kasuwa a kasuwar, Obenta Jude ya ce kawo yanzu gobarar ta kone rukunan kantuna biyu na shagunan kasuwar a layin Kano.

Ya ce kokarin ‘yan kwana-kwana na isa wurin jim kadan don kashe gobarar bai yi nasara ba saboda gobarar na ci gaba da ruruwa.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar kashe gobara, Engr Martin Agbili ya ce ba tare da bata lokaci ba ya tura jami'ansa yankin nan take bayan sanar da shi.

Ya ce: “Da misalin karfe 2:20 na dare 28-11-2022, Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Anambra, ta samu kiran tashin gobara a layin Kano da ke bayan babbar kasuwar Onitsha.

“Mun tura motocin kashe gobara da jami’an kashe gobara zuwa wurin da gobara ta tashi kuma suna aiki a wurin. Yanzu haka sun je sake ciko motar kashe gobara da ruwa sau na biyu.”

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post