Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
Wasu da ake kyautata zaton 'yan bindiga ne, sun kashe wasu mutanen kauye su hudu ciki har da wani sabon malamin makaranta da aka dauka aiki a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna.
Kashe-kashen ya faru ne a wasu kauyukan yankin da aka bayyana sunayensu da Gefe da Tudun Mare a karamar hukumar ta Kajuru.
Harin da aka kai Gefe ya yi sanadin mutuwar mutane uku, ciki har da na shugaban matasan kauyen a daren Lahadi.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa harin na biyu da ya auku a Tudun Mare ya yi sanadiyar kashe wani malamin makarantar mai suna Elisha Arziki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige ya ce zai kira wakilan daily trust din da zarar sun kammala bincike kan faruwar lamarin.
Inuwar Labarai RPT 001
