DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Kano Ta Janye Dokar Hana Bin Wasu Tituna Ga 'Yan Adaidaita.

Gwamnatin Kano ta sanar da janye dokar da ta haramta wa ’yan babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu zirga-zirga a wasu manyan titunan jihar.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta fitar a Yammacin wannan Larabar.

Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ya ce "mun janye dokar ne saboda al'umma sun koka akan dokar Kuma su ma Yan adaidaita sahu sun yi biyayya".

Al'umma da dama da ke bin wadannan tituna sun koka akan wannan doka inda aka ga yan makaranta da al'umma da dama suna tafiya a kafa.

Post a Comment

Previous Post Next Post