Kotun majistare a jihar Kano ta yi wa wasu matasa masu wallafa hotunan bidiyo a dandalin sada zumunta na Tiktok da Facebook bulala 20-20 tare da hukuncin biyan tara ta naira dubu 20 kowannensu da kuma share kotun na tsawon wata guda.
Hukuncin dai ya biyo bayan ta samun su da laifin bata sunan Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kokarin tada fitina a cikin al’umma,
Kazalika kotu ta ce su koma kan dandalin na tiktok din su yi bidiyon bai wa gwamna Ganduje hakuri kan bata masa suna.
Matasan Mubarak Isa Muhammad da aka fi sani da Mu, da Nazifi Muhammad Bala, na shirya gajeren bidiyon barkwanci, inda akasari suke kwaikwayon muryoyin wasu fitattun mutane.
Mabarak Unique Pidkin da abokinsa za kuma su share harabar kotun Norman Silance baki dayanta har na tsawon wata guda.
Lauyan da ya shigar da kara Barista Wada Ahmed Wada, ya shaida wa Majiyarmu cewa, an gurfanar da matasan ne a gaban kotun saboda laifukan da suka hada da bata sunan gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da kuma kokarin tayar da fitina.
