Daga Abdulnasir Yusuf Ladan
Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, a ranar Alhamis din da ta gabata, ya danganta matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a kasar, sakamakon karuwar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce gwamnati na kokarin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da jahilci a kasar nan.
An rawaito cewa ministan ya yi wannan jawabi ne a birnin tarayya Abuja a wajen taron ministoci na majalisar ilimi ta kasa karo na 66 (NCE), mai taken ‘Karfafa Tsaron Lafiya A Makarantun Najeriya Don Cimma Ilimin Ajandar Shekarar 2030.’
Ministan ya ce dole ne makarantu su kasance cikin aminci da tsaro ko ta halin kaka.
Ya kara da cewa: “Ina so in yi kira ga dukkan jihohi da su tashi tsaye wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu tare da samar da yanayin koyo da aminci ga dalibai da malamai.”
Karamin Ministan Ilimi, Goodluck Opiah, ya ce hare-haren da ake kaiwa makarantu, coci-coci, masallatai, tituna, tashoshin jiragen kasa, kauyuka da garuruwa suna kawo tarnaki ga harkar ilimi, tare da cin dunduniyar “tushen wanzuwar mu da kuma fallasa bangaren ga abubuwan da suka faru. ”
Ya ce wannan tabarbarewar na iya sanya harkar ilimi cikin rudani idan ba a yi wani abu cikin gaggawa ba.
Inuwar Labarai RPT 001
