Dan Jarida na Neman Diyyar Miliyan 100 bisa naushin da dan Siyasa ya yi masa a Kano

A ya yin da ake bikini ranar cin zarafin yan Jarida ta duniya a duk ranar 2 ga Nuwanbar kowace shekara. Wani Dan jarida a Kano ya fuskancin cin zarafin a wajen Dan Majalisar tarayya mai makiltar Tudun wada da Dogowa Hon. Alasan Ado Doguwa,

Lamarin dai ya faru ne bayan Doguwa ya kira Taron yan Jarida a gidansa domin maida martani akan rikicinsu da Dantakarar Mataimakin Gwamnan Kano Hon. Murtala sulen Garo, 

Danjaridar Mai suna Abdullahi Yakubu na Jaridar Leadership ya garzaga kotun Gyadi-gyadi karkashin jagorancin Halima Kurawa, inda ya nemi kutun ta kwato masa hakkinsa na naushinsa da Hon. Alasan Ado Doguwa ya yi a lokacin da yayi Taron manema labarai a gidansa,

A cewar Abdullahi Kunnesa fa ba ya ji sosai sai sama sama, inda ya garzagaya kotun tare da Neman kotun ta karbar masa Naira Miliyan 100, ta Kuma talilasta shi rubuta takardar Bada hakuri, 

Saura da me? abin jira a gani shi ne Amsa gayyatar da Hon. Alasan Ado Doguwa zai yi a gaban yan sanda na shiyya ta 1 da ke Sharada a Kano.

Post a Comment

Previous Post Next Post