Dan Takarar Shugaban Kasa A Jam'iyyar PDP Yaba da Tallafin Miliyan 50 Ga Wanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa A Hadejia.

Daga Abubakar M Taheer

Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar GCON, ya bada tallafin naira Miliyan 50 Ga Wanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa a fadar Mai martaba sarkin Hadejia.

Cikin jawabinsa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa sunzo jajantawa masarautar Hadejane ganin irin asarar dukiyoyi da rayuka da aka samu a sanariyar Ambaliya.

Atiku ya Kara da cewa ya bada tallafin naira Miliyan 50 Ga Yan kwanakin kula da Ambaliya Domin rabawa Wanda abun ya Shafa.

Dayake Jawabi Mai martaba sarkin Hadejia Alhaji Adamu Abubakar Maje CON, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara ta Atiku da Kuma Kira ga sauran Yan siyasa.
Mai martaba ya bukaci Dan Takarar Shugaban Kasa daya tsaya akwai liyafa ta musamman da masarauta ta shirya masa.

Cikin wadanda suka takewa Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku Abubakar GCON baya akwai Daraktan Yakin neman zaben jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, Sule Lamido CON, Amb Iliyas Damagun, Alhaji Adamu Maina Waziri, Sanata Deno Malaye.
Haka Kuma cikin tawagar akwai Dan Takarar gwamnan jihar Jigawa Alhaji Mustapha Sule Lamido, da mataimakinsa Dr.Babandi Ibrahim Gumel, Ambada Ibrahim Musa Kazaure, da Yan takarar Sanata Dr. Nuruddeen Muhammad, Alhaji Mustapha Khabeeb, Alhaji Bashir Adamu Jimbo.

Atiku Ya Sami tarba daga dimbin magoya bayansa daga cikin da wajen Jihar Jigawa dama jihohin dake makwabta ka da Jigawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post