Mutane 3 ne suka mutu a yayin gobarar kasuwa Badume a Kano

Hukumar kashe gobara jihar Kano, ta tabbatar da mutuwar wasu mutane uku sakamakon tashin wata gobara a kasuwar sayar da Tumatur da ke Badume a yankin ƙaramar hukumar Bichi.

Jami’in hulÉ—a da jama’a na hukumar Saminu Yusuf Abdullahi, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Juma’ar nan.

Sanarwar ta ce, ofishin hukumar na ƙaramar hukumar Bichi ne ya samu kiran gaggawa da misalin karfe 3:30 na dare daga wani mutum Malam Ibrahim Tsalha wanda ya bada rahoton tashin gobara a kasuwar ta Badume.

“Jami’an mu sun isa wurin da lamarin ya faru da misalin karfe 03:35 sai suka gano cewa, wani fili mai fadin mita 200 da tsawon mita 200 da ake yin amfani da shi a matsayin kasuwar tumatur ta Badume ya kama da wuta”

“Kimanin shagunan wucin gadi guda 100 ne a wurin da iftila’in ya faru, mutane uku sun maÆ™ale kuma har yanzu ba a tabbatar da sunayensu ba, akwai mace É—aya mai kimanin shekaru 35 da gurgu mai kimanin shekaru 30 sai kuma mutum na Æ™arshe mai kimanin shekaru 18, inji sanarwar.

 “Dukkan mutanen da tsautsayin ya rutsa da su, an ceto su ne ba a hayyacinsu ba, daga baya kuma aka tabbatar sun mutu, kuma mun damÆ™a gawarwakinsu a hannun Sufeto Mukaila Inusa jami’i a ofishin ‘yan sanda na Bichi”.

“Haka kuma mun yi nasarar ceto shagunan wucin gadi guda 100 a wurin” inji jami’in.

Sannan Saminu Yusuf Abdullahi ya ce, hukumar tana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar gobarar.

Post a Comment

Previous Post Next Post