Daga Abdurrazak Salisu Saheel
Tsarin "OpenDNS" babban tsari ne da yake taimakawa na'urorinmu musamman wayoyinmu ƙirar Android da yawanci muke amfani dasu kuma muke ziyartar shafuka kala-kala a Internet dasu, Already kasan cewa idan ka kunna data ɗin wayarka tahau kan Internet tana amfani da "Network Provider's DNS" wanda ake kira da "Internet Service Provider" (ISP), a taƙaice dai layin da kake amfani dashi MTN, Airtel da sauransu sune Network Providers ɗin wayarka, dan haka idan kayi Replacing "Provider's DNS ɗinka da "OpenDNS's" to duk wani bincike ko shiga wani shafi da zakayi da wayar naka akan Internet zaizo ne kai tsaye daga Filtered Servers na "OpenDNS's" wanda hakan zaiyi Blocking duk wasu bidiyoyin batsa (Porns) harda ma duk wasu abubuwa da zasu iya cutar da wayar naka, irinsu Malwares ko Virus da zai lalata wayar naka to wannan tsarin na "Open DNS" zaiyi blocking duk waɗannan mugayen abubuwa kafin suzo wayarka, sai ya tantance komai kafin yazo kan wayarka.
Sunada "IP Address" nasu, Addresses ɗin nasu sune kamar haka: 208.67.222.123
208.67.220.123.
Yadda zaka canja Android's DNS Settings ɗin shine kamar haka:
Farko kaje Setting ɗin wayarka, bayan ya buɗe sai kashiga wurin Wi-Fi zai baka Options da yawa na wasu Addresses, sannan ka tabbatar idan zakayi wannan aikin kayi shi da Wireless Network, bayayi da zallar Data. Daganan zakaga wayar taka tayi Connecting da ɗaya daga cikin Addressess ɗin sai ka danna Address ɗin da kayi Connecting Wireless dashi, Long Press zakayi, a wata wayar kuma sai kashiga wurin da aka rubuta "Advanced" sannan zakaga sauran Settings ɗin.
Dole akwai buƙatar mu mayar da "IP Settings" ɗin wayar daga "DHCP" zuwa "STATIC", bayan ka canza DHCP ɗin zuwa STATIC zakaga "Menu" ya canza ya nuno DNS Settings da suke akan wayar tareda baka damar kayi Editing ka canza "IP Address" da kakeso, karka damu, basai ka canza ba Already Android Device ɗin zai cike maka IP Address ɗin da ake buƙata ta DHCP, kawai "DNS Resolvers" ɗin mu zamu cike, wato wuraren da zakaga an rubuta "DNS 1" da kuma "DNS 2" sai kayi amfani da wannan 208.67.222.222 a matsayin DNS 1 ɗinka, DNS 2 shi ma sai kayi amfani da wannan 208.67.220.220, daganan sai ka danna wurin Save.
Shikenan yanzu ka kammala Updating "Device's DNS Server" na wayarka, kuma InshaAllah wayarka zata shiga cikin tsaro daga faɗawa cikin shafukan batsa da bidiyoyin batsa da kuma kare wayar daga Viruses da Malwares da suke lalata waya da leƙen asirin waya..
Note: Zaka iya amfani da hotunan da na saka wurin koyon yadda ake canja DNS ɗin.
Allah Yataimaka..🙏
Tags:
FASAHAR ZAMANI

