Daga Ibrahim Hamisu
Ma'aikatar sadarwa da cigaban tattalin zamani ta Nigeriya karkashin jagorancin Farfesa Ali Isah Pantami ta baiwa Cibiyar bayar da hoto akan fasahohin Zamani wato Engausa Global Tech Hub kambun karramawa a matsayin wacce ta yi fice a horar da Matasa fasahohin Zamani da kirkire-kirkire, wato wato THE BEST TRAINER a cikin abokan Hulda da hukumar NITDA,
An dai Mika lambar yabon ne a wani kasaitaccen biki da ya gudana a Abuja ranar Laraba 26-10- 2022, da yake jawabi yayin mika kyautar Ministan sadarwa da cigaban tattalin zamani Farfesa Ali Isah Pantami ya ce Cibiyar Engausa ita ce kan gaba a cikin cibiyoyin da ake hadin gwiwa da su wajen baiwa Matasa da sauran al'umma horo akan fasahohin Zamani harma da kirkire-kirkire Nigeriya,
Da ya ke karin haske akai shugaban Cibiyar Engausa Global Tech Hub Engr. Mustapha Habu Ringim ya bayyana Jin dadinsa da wannan tagomashi inda ya ce "Muna godiya ga Allah da ya sa wannan tafiya ta Engausa da har yasa Gwamnatin tarayya ta lura da cigaban da ake samarwa a cikin al'umma musamman alummar da take kasa wato (grassroot)da ma wadanda suka yi Digiri na biyu ta yadda tasirin horarwar ya kai ga shugabanni a gwamnatin tarayya kamar wannan hukuma ta NITDA da kuma ita kanta babbar Ma'aikatar sadarwa da cigaban Zamani Prof. Pantami ya ke jagoranta, wanda da ma Muna hadin gwiwa da ita NITDA wajen horar da Matasa, hakika mun gode da karramawar da akai mana".
Haka kuma wannan cibiya ta Engausa ta samu tagomashi inda aka sanyata cikin tawagar Gwamnatin tarayya da suka halacci babban taro a kasar Dubai inda shugaban Cibiyar kuma Sarkin Fasahar Hausawan Afirka, Engr. Mustapha Habu Ringim ya ce hakika Engausa ta karo Ilimi da dabaru a wannan tafiya ta yadda zata kara inganta harkokinta a Nigeriya da ma kasa baki daya.
Sannan wannan Cibiya ta Engausa ta samu nasar Samar da kayataccen dakin karatu na zamani don saukakawa dalibai yin karatu cikin sauki ta yadda Dalibai za su iya dauki littafi su karanta abinda aka koya masu a aikace su buÉ—e littafi su ganshi.


