'Yan Najeriya-Amurkawa Da Suka Yi Nasara A Zaɓen Tsakiyar Amurka.

Daga; Abdulnasir Yusuf Ladan 

Wasu ƴan Najeriya da suka fafata a zaben tsakiyar wa’adi na ƙasar Amurka sun yi nasara.

Shugabar hukumar ƴan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ce ta bayyana hakan a shafinta na tiwita a ranar Laraba tare da ta ya waɗanda suka yi nasara murna.

Ta wallafa a shafinta na tiwita cewa, “Wadannan Amurkawa ƴan Najeriya sun ci zaɓen da suka yi a Jihohi a daren jiya. Ina taya su murna duka."

Sun hada da Segun Adeyina, Gabe Okoye, Solomon Adesanya, Tish Naghise, Phil Olaleye, Carol Kazeem, Oye Owolewa da Esther Agbaje.

Inuwar Labarai RPT 001

Post a Comment

Previous Post Next Post