Daga Comrd Yusha'u Garba Shanga
A yau dubannin iyaye ne suka fito a ƙofar babban makarantar sakandari ta tarayya dake garin Birnin Yauri Jihar Kebbi domin nuna rashin jindaɗinsu abisa sauran yaransu dake tsare a hannun 'yan ta adda fiye da shekara ɗaya da watanni.
Biyo bayan zanga-zangar lumanar tare da jawabin da iyayen suka bayyanar ayau, domin nuna rashin jindaɗinsu ganin yadda gwamnatin tarayya dakuma ta jiha tayi marus tare da kunnen uwar shegu babu wani zance mai ƙarfi dangane da bayyanar yaransu.
"Acikin jawabin maman safiya (jargaɓa) ɗaya daga cikin iyaye mata dasuka bayyana damuwarsu, ta bayyana irin ƙalubalen da iyayen yaran ke fuskanta cewa wasu sun ɗauki cutar hawan jini, wasu sun kasa samun sukuni tare da shiga yanayi na marar daɗinji, kwanciya barci gagararsu yake na rashin sanin wani irin haline yaransu ke fuskanta.
Sunkara kira ga gwamanti tare da cewa waɗannan yaran iyayensu na cikin wani hali na buƙatar ganinsu
Safiya Idris
Fa'iza Ahmed
Bilhah Musa
Elizabeth ogechi nwafor
Rahama Abdullahi, da sauran su
Allah ya bayyanar daku tare da lafiya mai inganci, matsayar mu da gwamnati shine susan da irin halayen da muke, babu labari bale jin ɗuriyar yaranmu, meye matsayar sauran yaranmu dake hannun masu garkuwa da mutane?.


