Daga Abdulnasir Y. Ladan
Dattijon mai suna Malam Isah Ibrahim, mai shekaru 67 yana noma albasa sama da buhu 100 da masara sama da buhu 100, ya na samun akalla ribar miliyan biyu cikin kowacce shekara kafin fara rikicin Boko Haram, rikicin Boko Haram ya tilasta masa tserewa daga garin Baga ba tare da ya dauki ko sisin kobo daga dukiyar sa ba a shekarar 2014.
Yanzu haka Malam Isa ya koma sana'ar tura kurar ruwa inda yake samun abin da zai sanya a bakin salati.
Inuwar Labarai RPT 001
